Accessibility links

Ziyarar Buhari Ta Farko Zuwa Nijar Bayan Rantsarwa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Ranar Rantsar Da Shi.

Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da aka rantsar a ranar 29 ga watan da ya gabata na Mayu shekarar nan ta 2015 zai kai ziyararsa ta farko zuwa Jamhuriyar Nijar.

A matakan farko domin neman hanyar dakile matsalar boko haram, shugaba Buhari zai kai ziyarar ne zuwa Nijar har ma da wasu makwabtan Najeriya. Mutane sun daga girar saman idanuwansu game da dalilan da Buharin ya hanga zai kai wannan ziyara.

Musamman ma da a baya shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya nuna cewa ba a taba wani zaman a zo a gani ba tsakanin kasashen biyu ba don magance matsalar ba. Boko Haram dai na daya cin manyan matsalolin tsaro a tsakanin wadannan kasashe.

Shehu Garba shine mai magana da yawu shugaban kasar wanda ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka a hirarsu da Bello Galadanchi, inda shugaban yake shirin zuwa da lokacin tafiyar tasa.

XS
SM
MD
LG