Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kalubalanci Tinubu Kan Shirun Da Ya Yi A Lokacin Da Aka Far wa ‘Yan Arewa A Kudu


Daga dama, Tinubu, Ganduje da Nastura (Instagram)

Ga dukkan alamu, ziyarar da tsohon gwamnan jihar Legas Ahmed Bola Tinubu ya kai Kano inda aka shirya taron tattaunawa don zagayowar ranar haihuwarsa yayin da ya cika shekara 69, ta ta da kura.

Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, ta kalubalanci jagoran jam’iyyar APC mai mulki Sanata Ahmed Bola Tinubu kan shirun da ya yi a lokacin da aka far wa ‘yan arewacin Najeriya a kudancin kasar.

‘Yan arewa da dama aka kashe tare da lalata musu dukiyoyi a lokacin zanga-zangar Endsars da aka yi a watan Oktoban bara a kudancin kasar, - abin da gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriyar ta ce ya kamata a ce Tinubu ya fito ya yi tir da lamarin a lokacin.

Karin bayani akan: Sanata Ahmed Bola Tinubu, Kano, Shugaba Muhammadu Buhari, APC, Nigeria, da Najeriya.

“Lokacin da aka yi zanga-zangar Endsars, mutanen arewa ba su ci ba, ba su sha ba, haka kawai aka far musu aka rika karkashe su ana kone musu dukiyoyinsu a kudancin Najeriya – duk ina su Bola Ahmed Tinubu suke lokacin da aka yi wa mutanen arewa irin wannan abin? Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya Nastura Ashir Shariff ya ce a wani bidiyo da VOA ta samu.

Kalaman kungiyar, martani ne ga ziyarar da tsohon gwamnan jihar ta Legas yake kan yi a wasu jihohin arewa, inda rahotanni suka nuna cewa yana Kano kuma a nan za a yi taron bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)
Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)

A ranar Lahadi, Tinubu ya kai wa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero ziyara a fadarsa karkashin jagrancin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Kungiyoyin har ila yau sun kalubalanci shirin da ake yi na gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar Tinubu a gidan gwamnatin jihar ta Kano.

“Kowa ya san wannan siyasa ce kawai, mutanen da ya kamata a ce an fara yi wa irin wannan taro su ne, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ko Alhaji Kabiru Gaya, ko Rabiu Musa Kwankwaso, ko Malam Ibrahim Shekarau.”

“Idan maganar girmamawa ce, a jihar Kano ai ba mu yi mutane irinsu Malam Aminu Kano ba, su marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule, Murtala Muhammad, Gen. Sani Abachi, da mutane irinsu Magajin Gari Inuwa Wada, da irinsu Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero – me Tinubu ya yi wa mutanen Kano ko gwamnatin jihar Kano, har da za a yi amfani da gidan gwamnati a yi masa wannan abu a nan.”

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu

A cewar Nastura, wannan ba ziyara ba ce, “kaddamar da yakin neman zabe ne karkashin jam’iyyar APC, kuma ana so a yi amfani da wasu dillalai na siyasa,” don cimma wannan buri.

“Da ma mun fada, kamar sati uku da suka, wuce na yi wannan bayanin, na ce, akwai wasu dillalai da ake magana da su a arewacin Najeriya, wadanda shi Sanata Ahmed Bola Tinubu yake amfani da su cewa za su zo su sayar da shi a arewa, saboda haka, ku yi watsi da shi da wadanda suka zo da shi,” in ji Nastura.

Sai dai a martanin da ta mayar gwamnatin Kano ta ce, kawo taron muhadarar zagayowar ranar haihuwar Tinubu, mataki ne na kara nunawa jama’a matsalolin da za a tattauna akai a wajen taron sun shafi Najeriya ne baki daya, ba wai an takaita zuwa ga jihar Legas a ko da yasuhe ba.”

“Ba wai gwamnatin jihar Kano ba ce ta ba da wani kudi aka dauki nauyin wannan taro ba, illa iyaka abin da gwamnatin jihar Kano ta yi shi ne ta ba da wuri, wato masauki na Coronation Hall da ke cikin gidan gwamnati.” In ji Babban Darektan hulda da manema labarai da jama’a Aminu Kabir Yassar.

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Yassar ya kara da cewa, wannan taro an saba yin shi, “wannan kusan shi ne kusan karo na 12 da ake gudanarwa da wannan muhadara, inda ake tattauna matsaloli da suke damun al’uma, a kuma ba hukumomi shawara kan yadda za a samu maslaha.”

Ya kara da cewa, “ba wai bukukuwa ake yi a yi na kide-kide ana ciye-ciye ana shaye-shaye ba.”

Dangane da korafin da kungiyoyin arewacin Najeriya ke yi don gudanar da taron a fadar gwamnatin Kano, jami’in gwamnatin ya ce Kano ta banbanta da Legas.

“A Kano ba mu da manya-manyan wuraren taruka, wadanda za su iya cin jama’a kamar yadda ake da su na haya a jihar Legas, shi ya sa a jihar Legas, ba a gudanarwa a gidan gwamnati. Ka ga Coronation Hall da muke da shi a gidan gwamanti da muke da shi, akalla zai ci mutum dubu daya da wani abu, ba na tsammanin muna da wani wuri da zai iya cin kamar wannan adadi.”

Yayin kuma da yake mayar da martani kan zargin cewa ana kokarin tallata Tinubu don cimma burins ana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, Yassa rya ce, “zargi ko maganganu irin wadannan, abubuwa ne da za a iya kiransu a matsayin gishiri na dimokradiyya.”

Shi dai Tinubu bai fito fili ya bayyana cewa yana da burin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ba.

Amma masu lura da al’amuran siyasa sun ce zai tsaya takarar shugaban kasar a shekara ta 2023.

Ko da yake, rahotanni sun ce a lokacin da ya je fadar Sarkin Kano a ranar Lahadi, Tinubu ya kwatanta ziyarar tasa a matsayin wani, “yunkuri na kara hada kan kasa da kuma ganewa idonsa irin ci gaban da aka samu a jihar ta Kano.”

XS
SM
MD
LG