Dakarun Iraqi Sun Kwato Wata Ma’aikatar Gwamnatin Birnin Fallujah

Sojojin Iraqi da Amurka ke marawa baya ta kai hare hare ta sama, sunyi kokarin korar kungiyar ISIS daga tsakiyar birnin

A yau Juma’a dakarun Iraqi sun kwato wata ma’aikatar gwamnatin birnin Fallujah daga hannun mayakan kungiyar IS, bayan kwashe kusan wata ‘daya ana bata kashi kafin a kai ga ginin.

Sojojin Iraqi da Amurka ke marawa baya ta kai hare hare ta sama, sunyi kokarin korar kungiyar IS daga tsakiyar birnin, acewar shugaban ‘yan sandan kasar Iraqi, wannan wata alamace ta nasara ga sojojin hadin guiwa.

Kungiyar IS sun kwace garin Fallujah a shekara ta 2014, amma bayan kwashe sama da wata ‘daya ana mummunan fada, sojojin Iraqi sun sami damar kwato kusan rabin birnin. A yunkurinsu na baya bayannan, dakarun sun shiga birnin wajen karfe 6 na safe inda kuma ba wata cijewa da suka fuskanta daga mayakan na ISIS.

Jami’an tsaro sun ce yawancin mayakan na kungiyar IS sun arce daga birnin a wannan makon, sanye da tufan fararen hula don batar da kama.