A BARI YA HUCE: Labarin Addu'ar Wani Banufe Akan Bahadeje A Makka

Baba Yakubu Makeri da Grace Alheri Abdu

Washington, D.C. - A wannan shirin za ku ji labarai biyu na wani banufe da ya je Makka yana addu'a, sai wani bahadeje ya tsaya bayansa yana cewa ka ninka min duk abin da banufen nan ke roka, sai banufe ya ce Allah ka nakasa min idona daya wato bahadeje ya makance kenan.

Sai kuma labarin wanda ya je sayen ragon layya, bayan kammala ciniki, mai sayen rago ya kirga kudi kafin ya bayar sai rago ya fizge kudin ya tattauna ya hadiye, tambaya itace, wanene ke da bashi?

Saurari cikakken shirin da Alheri Grace Abdu da Baba Makeri suka gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

A BARI YA HUCE: Labarin Addu'ar Wani Banufe Akan Bahadeje A Makka