A Bari Ya Huce: Labarin Mahaukaci A Kasuwa-Oktoba 24, 2020

Alheri Grace Abdu

Wani mahaukaci ne ya shiga kasuwa yana tsula gudu,yana cewa " gasu nan sun taho,gasu nan sun taho mutane suka yi ta gudu,kasuwa ta hargitse ana ta gudu.

Can wasu gayu bayan sun sha gudu sun gaji,sai suka hango wannan mahaukacin shi ma yana ta nishi yana haki ya gaji libis. Sai suka matsa kusa da shi suka ce mashi wai su waye suka taho ne?

Sai mahaukacin yace 'yan NEPA ne naga sun nuho kasuwan nan da mota har da tsani shi ne na ke kokari in janye hankalin su kada su bi mutane sun yanke masu wuta.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce: Labarin Mahaukaci a kasuwa-29:00"