Amurka Tana Zargi Iran Da Kai Hari A Kan Jiragen Dakon Mai

Jirgin dakon mai Kokuka Courageous

Sakataren tsaron Amurka Pat Shanahan yace Amurka tana kokarin kulla wani babban hadin kan kasa da kasa a kan batun Gabas ta Tsakiya game da harin da aka kaiwa jirgen dakon mai a kan tekun Oman.

"Lallai muna bukatar daukar karin matakai, saboda idan al’amura suka ci gaba da rincabewa, amma kuma yakamata mu fadada neman hadin kan kasashe a kan wannan batu" inji Shanahan a jiya Juma’a.

Amurka tana dora laifin kai harin ne a kan kasar Iran kuma sojoji sun fitar da wani hoton bidiyo dake nuna wasu mutane a cikin wani jirgin Iran mai sintiri suna fitar da wasu abubuwar fashewa a cikin jirgin dakon man mai suna Kokuka Courageous.

Wani kamfanin jiragen ruwa na kasar Japan Kokuka Sangyo ne ke mallakar jirgi daya na dakon man kana kamfanin Front Altair na kasar Norway ne ke mallakar dayan jirgin.

Kamfanin dillancin labaran Iran tace sojojin ruwan Iran sun ceto ma’aikatan jiragen ruwan dakon man 44.