Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jiragen Ruwa Biyu Sun Kone A Kogin Oman


An lalata wasu manyan jiragen ruwa guda biyu, masu jigilar man fetur da aka kaiwa hari a yau Alhamis, a kogin Gulf na Oman, wata muhimmiyar mashigar zirga-zirgar jirage dake bakin gabar teku a Iran.

Hukumar sufurin jiragen ruwa ta kasar Norway tace an ji kararraki har guda uku na fashewar wani abu mai kama da nakiya, akan jirgin ruwan kasarta mai suna “Front Alter”, jim kadan bayanda aka kai makamancin wannan farmakin akan wani jirgin ruwa mallakar kasar Singapore da ake kira “Courageous.”

Bataliyar sojan Amurka ta 5 dake a Baharain tace ta soma kai agaji bayanda ta sami sakonnin gaggawa daga jiragen biyu, wadanda aka ce sun kama da wuta a cikin tekun.

Haka kuma kamfanin dillancin labaran IRNA na gwamnatin Iran yace sojan ruwa na Iran sun ceto ma’aikata 44 na jiragen.

Har zuwa yanzu dai ba tabbas akan nau’in makaman da aka yi anfani da su wajen kai farmakin akan jiragen biyu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG