An Gudanar da Taron Addu'a a Gombe Saboda Alhazan da Turmutsitsin Saudiya Ya Hallaka

Turmutsitsin Saudiya: Masu aikin ceto

A garin Gombe an gudanar da taron addu'a na kasa saboda maniyattan kasar da suka halaka a turmutsitsin Saudiya yayinda suke jifan shedan

An gudanar da taron ne domin neman Allah ya gafartawa wadanda suka rasa rayukans sakamakon turmutsitsin.

Mutanen da suka mutu sun hada da talakawa, manyan ma'aikata, 'yan kasuwa, jami'an gwamnati da 'yan jarida.

Farfasa Tijjani El-Miskin na cikin mutanen da suka rasa rayukansu.

Wani Sheriff Muhammad Danlami abokin Farfasa El-Miskin kuma shugaban wadanda suka shirya addu'ar yace sun samu labarin cewa 'yanuwan da yawa sun samu shahada a Saudiya saboda haka suka ga ya zama wajibi su yi masu addu'o'i na neman samun gafara.

Danlami ya yi watsi da batun cewa kasar Saudiya ce zata binciki kanta akan abun da ya faru.Yace kamata ya yi a ce duk kasar da ta rasa wani nata to dole a sata cikin biciken saboda tabbatar da gaski. Idan Saudiya ke da laifi to ta nemi gafara. Idan kuma bata da laifi to kowa sai ya rungumi kadara.

Dangane da Bilkisu Yusuf fitacciyar 'yar jarida da ta rasu a turmutsitsin wani Bashir Hassan Abubakar dan jarida yace tun yana makaranta yake bibiyan Bilkisu Yusuf. Yace su dake tasowa yanzu sun yi babbar rashi.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar da Taron Addu'a a Gombe Saboda Alhazan da Turmutsitsin Saudiya Ya Kashe - 3' 16"