Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'ayi Nazarin Tsarin Ayyukan Hajji A Saudiyya


Muslim pilgrims and rescuers gather around the victims of a stampede in Mina, Saudi Arabia during the annual hajj pilgrimage on Thursday, Sept. 24, 2015.
Muslim pilgrims and rescuers gather around the victims of a stampede in Mina, Saudi Arabia during the annual hajj pilgrimage on Thursday, Sept. 24, 2015.

Sarki Salman na kasar Saudiya ya bada umarnin nazarin tsarin ayyukan hajji bayan turmutsutsun da aka yi a bayan birnin Makka da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane dari bakwai da goma sha bakwai, wadansu sama da dari tara kuma suka ji raunuka.

An nuna hotun bidiyon gawarwakin mutane a kasa, da wadanda suka ji raunuka wadansu kuma suna kuka a Minna dake tazarar kilomita biyar da birnin Makka.

Mahajjata suna zuwa wurin ne domin jifar shaidan, aikin ibada na karshe kafin bukin sallah.

An yi jerin gwano ana fuskantar zuwa wuri guda ne da rana, kafin wani rukunin mahajjata ya juya ya fara komawa, abinda yasa aka rika karo ana tattake mutane maza da mata, tsofaffi da majiya karfi.

Wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya ya bada rahoto cewa, turmutsutsun ya faru ne a wurin ayyukan ibada dake Mina, inda aka kafa sama da tantuna dubu dari da sittin domin masu aikin hajji.

Wannan turmutsutsun shine sanadin asarar rayuka na biyu da aka samu wannan watan, bayan gocewar wata kugiyar daukar kayan gine gine da tayi sanadin mutuwar mutane dari da tara a birnin Makka bana.

XS
SM
MD
LG