Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da korar ‘yan sandan da ake zargin sun harbe wasu matasan Fulani makiyaya, kan sunki basu na goro, korar tasu dai ta biyo bayan samunsu da laifi a rahotan kwamitin binciken da aka kafa game da lamarin.
Haka nan kuma an rage wasu jami’an ‘yan sanda biyu mukami da suma aka samesu da laifi a ta’asan kisan makiyayan, DSP Othman Abubakar, dake zama kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa yayi karin haske game da matakin da aka dauka, yace, “kwamishinan ‘yan sanda da musamman inspector janal na Najeriya bai ji dadin wannan al’amarin daya faru ba, kuma ya bada umarnin a dauki matakin daya kamata,” yakuma cigaba da shaida mana cewa mutanen nan biyu dake da hannu cikin batun harbin Fulanin an sallamesu daga aiki, kuma za’a gabatar dasu gaban kotu in an dawo daga yajin aikin da kotu ke ciki.
A martanin data maida hadakar kungiyar makiyaya ta Najeriya Miyatti Allah ta yabane da wannan mataki, Alhaji Sanusi Bara wani Jami’in kungiyar ne a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya wanda yace, “gaskiya sun yi dai dai da korar su, domin basu dace ace suna cikin ‘yan sandan Najeriya ba, domin aikin ‘yan sanda shine kula da rayuka da dukiyar mutane, yanzu kuma ya zamanto sune ke kashe rayuka. To karar su da akayi yayi dai dai, kuma mutanen mu Fulani dayawa sunyi farin cikin ganin yadda al’amarin ya kasance.”
Batin yau bane jami’ai a Najeriya sukayi kaurin suna wajen karbar na goro a hannun jama’a, lamarin da kan bata sunan kasar a idon duniya.
Your browser doesn’t support HTML5
Korar 'Yan Sanda Kan Kisan Makiyaya Fulani - 2'55"