Babu Sauran Tattaunawa Da Sudan Ta Kudu, In Ji Shugaba Omar al-Bashir

Mutane su na daga tutar Sudan ma sojoji a lokacin wani maci na murnar nasarar da suka samu a kofar ma'aikatar tsaro dake Khartoum ranar 20 Afrilu, 2012.

Shugaban na Sudan ya fadawa sojojin kasarsa cewa babu abinda Sudan ta Kudu ta fahimta illa bindigogi da harsasai.

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan yace babu sauran tattaunawa da Sudan ta Kudu, a yayin da shaidu a Kudu suke fadin cewa jiragen saman yaki na Sudan sun kai hare-haren bam.

Shugaba Bashir ya bayyana wannan ga sojojinsa jiya litinin a lokacin da ya ziyarci Heglig inda ake hakar mai, wanda kuma sojojin Sudan suka kwato daga hannun sojojin Sudan ta Kudu a ranar jumma'a.

Shugaba Bashir yace babu abinda Sudan ta Kudu ta fahimta im ban da bindigogi da harsasai.

Jami'an gwamnati da kuma shaidu a Sudan ta Kudu sun ce jiragen saman yaki na Sudan sun kai hari cikin Jihar Unity a Sudan ta Kudu jiya litinin, suka kashe mutane uku, ciki har da wani saurayi. An jefa bama-baman ne a ciki da kuma kewayen garin Bentiu dake bakin iyaka.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi tur da hare-haren bam din da Sudan ta kai, ya kuma yi kira ga gwamnati a Khartoum da ta kawo karshen wannan farmaki nan take.