Bom Ya Tashi A JIhar Adamawa

Hoto Harin Bam a Masallacin na Kano, Nuwamba 28, 2014.

wani bom da aka binne a kusa da bakin hanya,ya fashe a kauyen Lugdira,dake yankin Maiha wanda yayi sanadiyar asarar rai da kuma raunata wasu ,yayin da suke jin dumi a safiyar yau lahadi

Rahotanni daga arewacin jihar Adamawa,na cewa wani bom da aka binne a kusa da bakin hanya,ya fashe a kauyen Lugdira,dake yankin Maiha wanda yayi sanadiyar asarar rai da kuma raunata wasu ,yayin da suke jin dumi a safiyar wannan rana ta lahadi.

Cikin kwanakin nan ne dai dakarun sojojin kasar,dake samun tallafin yan sakai na maharba da yan kato da gora,wato civilian JTF,suka sami nasarar fatattakar mayakan Boko Haram a yankunan Maiha,Mubi,Hong da kuma Gombi,wanda hakan yasa ake tunanin kafin korarsu tana yuwa,mayakan sun daddasa bama-bamai a wasu wurare da suka yi sansani a baya.

Ga rahoton da wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya aiko mana daga Yala fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Bom A JIhar Adamawa-3:08