Burin 'Yan Najeriya Kan Shekara 2014

Shugaban Najeriya da wasu 'yan kasar

Yayin da karshen shekarar 2013 ke karatowa 'yan Najeriya sun soma burin abubuwan da suke so su gani a shekarar 2014 da yau saura kwana biyar kacal mu shigeta idan Mahalicinmu Ya yadda.
Cikn 'yan kwanaki kadan shekarar 2013 zata shude tare da harsashen jama'ar kasa. To ko menene jama'a suke harsashen son gani a sabuwar shekara mai zuwa?

Wasu mazaunan babban birnin Najeriya wato Abuja sun bayyana abubuwan da suke fata su gani a sabuwar shekarar. Sani Sale mai magana da yawun gwamnan jihar Nasarawa ya ce yana fatan a sabuwar shekara mai zuwa za'a samu ingantacen tsaro a kasar sabo da abun da ya fi damun jama'a a wannan shekarar shi ne rashin tsaro. Idan babu ingantacen tsaro babu yadda harkokin siyasa zasu tafi yadda ya kamata. Sabo da haka abun da shi yake son gani cikin sabuwar shekarar shi ne samun tsaro a duk fadin Najeriya musammana a jiharsa ta Nasarawa inda aka samu rigimar kungiyar Mbatse.

Musibahu Lawal Didi shugaban guragu na kasa da kungiyar wadanda suka kamu da shan inna na kasa, kuma dan kasuwa a Abuja ya ce burin shi shi ne ya ga cewa kudirin da aka yi kan nakasassu domin inganta rayuwarsu da jin dadinsu ya zama doka. Abu na biyu yana son a yi masu adalci cikin kasafin kudin da aka yi na shekara mai zuwa abubuwan jin dadin jama'a da aka tsara za'a yi a tabbatar an yi ba tare da karkata kudaden zuwa wani wuri ba, musamman abun da ya shafi masu lallurar nakasa.

Hajiya Amina Abubakar shugabar sashen matasa a jam'iyyar PDP ta ce burinta shi ne matasa su samu abun yi a Najeriya. Matasa sun gama karatu amma babu aikin yi. Matasa mata da zara an ce babu aikin yi to sun shiga wani kangi ke nan. Ta ce tana son ta ga mata matasa sun samu abun yi, sun samu aikin yi.

Abdullahi Shifkau daga jihar Zamfara yana fatan Allah ya kawo canji na kwarai, Allah ya taimaki kasar da shugabanni na gari.Ya ce fatarsu ke nan domin a gaskiya suna cikin wani hali ba wai irinsu ba a'a duk fadin kasar. Ya ce duk mai niyar shugabanci na gari koshi wanene Allah ya taimakeshi.

Abubakar Abdullahi daga kihar Kano ya ce fatan da suke da shi a shekarar da za'a shiga shi ne zaman lafiya domin idan babu zaman lafiya babu wani cigaban da za'a samu. Ya kira shugabanni su ji tsoron Allah. Duk abubuwan da zasu yi su yi cikin tsoron Allah domin akwai ranar da Ubangiji zai tambayemu duk abubuwan da muka yi tun daga haifuwarmu har zuwa rasuwarmu. Ya ce shugabanni su duba suga abun da talakawa ke ciki. Idan mutum ya je kauye zai tausayawa talakawa.

Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Burin 'Yan Najeriya Kan Shekarar 2014 - 3:40