Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kashe 'Yan Yakin Sa Kai Hamsin


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ya yi ikirarin kashe a kalla 'yan yakin sa kai hamsin a jihar Borno.Rundunar sojan Nigeria tace sojojinta sun kashe akalla 'yan yakin sa kai hamsin a sumamen da suka kai na farauto wadanda suka kai mumunar hari akan barikokin soja a arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Nigeria, Janaral Chris Olukolade ya fada a jiya Talata cewa sojoji goma sha biyar da farar hula guda biyar suna daga cikin wadanda aka kashe a harin da aka kai birnin Bama a ranar Juma'a.

Wannan birnin yana jihar Borno ne, daya daga cikin jihohin da aka ayyana dokar ta baci aka tura karin sojoji domin yaki da yan yaki sa kai.

Kungiyar Boko Haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hari akan wani sansanin soja a birnin Maiduguri a farkon wannan watan.
XS
SM
MD
LG