Chloé Zhao Ta Kafa Tarihi A Bikin Ba Da Lambar Yabo Na Oscar

Chloe Zhao

Zhao ta lashe kyautar lanbar yabo na Oscar a matsayin babban darakta na "Nomadland," ta kuma zama mace ta biyu kuma mace ta farko da ba farar fata ba da ta lashe kyautar.

Shekara ɗaya tilo a cikin tarihin lambar yabo Oscar da aka samu mata biyu su ka shiga takara, Zhao da kuma Emerald Fennell, daraktan " Promising Young Woman ". Mata bakwai ne kawai aka taba tantancewa.

Wannan shine lambar yabon Oscar na farko ga Zhao mai shekaru 39, wanda aka haifa a Beijing kuma ta tafi makarantar koleji da makarantar fina-finai a Amurka. "Nomadland" shine shiganta na uku.

Daniel Kaluuya ya samu nasarrar kyautan Oscar a matsayinsa na wanda ya jagoranci wasan kwaikwayo. Ya kuma karba.

Kaluuya ya lashe lambar yabo ta farko a daren Lahadi don wasa daya daga cikin manyan fina-finai biyu a cikin " Judas and the Black Messiah."."

Fim din Denmark, wanda Thomas Vinterburg ya bayar da umarni, ya ci kyautar Oscar don mafi kyawun fim na duniya.

Wannan shi ne karo na hudu da wani fim daga Denmark ya yi nasara a rukunin. Na ƙarshe kafin shi, shine " In a Better World " a cikin 2010.