DOMIN IYALI: Gwagwarmayar Matan Najeriya Da Neman Wakilci A Zaben 2023-Janairu, 26 , 2023

Alheri Grace Abdu

Yau ya rage saura makonni hudu a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun tarayya a Najeriya, makonni biyu bayan nan kuma a gudanar da na gwamnoni da majalisun jihohi.

Sai dai duk kokarin da mata su ka yi na ganin wannan karon ba a bar su a baya ba, hakar su bata cimma ruwa ba, kasancewa ba su sami wakilcin da suke nema ba.

Batun da zamu fara nazarta ke nan a wannan makon a shirin Yau shirin Domin Iyali.

Bakun da mu ka gayyata domin neman mafita su ne, Hajiya Binta Musa shugabar kungiyar hadin kan mabiya addinai dabam- daban reshen jihar Plato, da Ambassada Rhoda Godwill Jahota, shugabar Kungiyar Mata Kirista a jihar Plato, da Dorcas Lenkat Yusuf shugabar gamayyar Kungiyar Ma’aikatan gwamnati a jihar Plato mai barin gado, sai kuma Ambassada Ridwan Jimat Imam, malami karkashin kungiyar Jama’atu Nasril Islam.

Saurari shirin da wakiliyarmu Zainab Babaji ta jagoranta:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Gwagwarmayar Matan Najeriya Da Neman Wakilci A Zaben 2023