DUNIYAR AMURKA: Amurka Na Shirin Dakatar Da Sayar Da Makamai Ga Saudiyya Saboda Ta Goyi Bayan Rasha, Oktoba 14, 2022

Mahmud Lalo

Kazalika shirin ya duba matsayar da kwamitin majalisar dokokin Amurka ya cin ma na aika takardar gayyata ga tsohon shugaba Amurka Donald Trump don ya ba da bahasi kan harin da aka kai ginin majalisar a 2021.

'Yan Democrats da ke Majalisar Dokokin Amurka na shirin samar da wata doka da za ta dakatar da sayar da makamai ga Saudiyya bayan da masarautar ta marawa Rasha baya kungiyar kasashen da ke samar da mai ta OPEC plus, ta rage adadin man da za a rika hakowa a wani taro da ta yi a makon da ya gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Amurka Na Shirin Dakatar Da Sayar Da Makamai Ga Saudiyya Saboda Ta Goyi Bayan Rasha - 6'00"