DUNIYAR AMURKA: Mahaukaciyar Guguwar Ida - Satumba 03, 2021

Mahmud Lalo

Akalla mutum 40 ne suka mutu a tsakanin jihohin New York, New Jersey, Pennsylvania da Connectitcut a ranar Laraba, bayan da mahaukaciyar guguwar da aka wa lakabi da Ida ta haddasa ambaliyar ruwa a wadannan jihohi, lamarin da har ila yau, ya tsayar da ala’amura cak a New York, birnin da ya fi ko ina yawan jama’a a Amurka.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Mahaukaciyar Guguwar Ida - 6'25"