ECOWAS Ta Nada Issouhou Mahamdou A Matsayin Jami'in Tattaro Kudaden Yaki Da Ta'addanci

Shugaba Issouhou Mahamadou

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta nada tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou da shugaban Nana Akufo Addo na Ghana a matsayin gwarazan tattara kudaden yaki da ta’addanci.

Matsalar tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da shugabanin kasashen CEDEAO suka tattauna akansu a yayin taron da ya gudana a karshen mako a kasar Ghana.

Hakan ya bada damar kira ga kasashen da ba su biya kudaden gidauniyar yaki da ta’addanci da ya wajaba a wuyansu da su gaggauta sauke wannan nauyi domin kara jan damarar yaki da ‘yan ta’adda.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Taron ya yanke shawarar dorawa Tsohon shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou da shugaban kasar Ghana Nana Akufo Ado nauyin nemo kudaden da za su taimakwa a cimma burin da aka sa gaba a fannin tsaro a matsayinsu na gwarazan da CEDEAO ta gamsu da jajircewarsu wajen tattaro kudaden yaki da ta’addanci.

A Nijar, wannan batu ya dauki hankalin ‘yan siyasa. Sai dai wani kakakin ‘yan adawa Alhaji Doudou Rahama na yi wa abin wata fassara ta daban.

Barazanar tsaron da yanayin kasar Libya ke yi wa kasashen Afrika ta yamma wani abu ne da kungiyar CEDEAO ta bukaci kasashen duniya su dube shi da idon rahama ganin yadda sojojin haya suka fara yukurin kutsawa kasashen dake makwaftaka da kasar Libyar.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ECOWAS Ta Nada Tsohon Shugaban Nijer A Matsayin Jami'in Tattaro Kudaden Yaki Da Ta'addanci