Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen CEDEAO Sun Kudiri Murkushe Ta'addanci A Yankin Sahel


ECOWAS
ECOWAS

Taron shugabannin kasashen Afirka ta yamma mambobin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS, da ya gudana a birnin Ouagadougou ya bayyana shirin tattara biliyan daya na dalar Amurka, domin karfafa matakan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Taron na birnin Ouagoudougou dake matsayin na gaggawa, ya mayar da hankali ne wajen neman hanyoyin magance matsalolin ta’addanci a yankin Sahel. Lamarin da ya sa shugabannin kungiyar CEDEAO na yanke shawarar harhada kudaden tunkarar wannan kalubale, kamar yadda suka bayyana a sanarwar karshen taro.

Ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar Kalla Hankourao, na cewa kasashen ECOWAS sun yanke shawarar tattara biliyan daya na dalar Amurka domin murkushe ta’addancin da ya addabi yankin Sahel. Mafari kenan aka bukaci hadin kan kasashen Chadi da Mauritania a wannan sabuwar tafiya a karskashin tsarin fasalin aiyukan da kungiyar ta kudirta daga shekarar 2020 zuwa 2024.

Halin da ake ciki a kasar Libya wani abu ne da shugabannin kasashen Afirka mambobin CEDEAO suka ce ya na mayar da hannun agogo baya, a yunkurin da aka sa gaba wajen kawo karshen aiyukan ta’addanci a yankin Sahel.

Musanyar bayanai ba tare da wani jinkiri ba a tsakanin kasashen ECOWAS, da zurfafa nazarin hanyoyin kafa rundunar hadin gwiwar kasashen Yammacin Afirka, tare da batun asusun farfado da yankunan da rikicin ta’addanci ya shafa, na daga cikin shawarwarin da taron na Ouagadougou ya tsayar a watan Disamba dake tafe, na shugabannin kasashen Yammacin Afrika da zasu hadu a Abuja domin saka hannu akan takardun zartar da wannan kudiri na harhada hancin biliyan daya na dalar Amurka.

Ga caikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG