Firayim Ministan Pakistan Zai Ziyarci Afghanistan Yau

Firayim Ministan Pakistan Shahid Khaqan Abbasi

A wani yunkuri da ka iya zama kokarin neman zaman lafiya tsakanin kasashen dake makwaftaka da juna ta hanyar shawo kan 'yan Taliban dake kasashen biyu inda suke ta'addanci ziyarar ka iya zama mafita

Firayin Ministan Pakistan Shahid Khaqan Abbasi, ya yi shirin kai ziyarar aiki a Afghanistan a yau Jum’a domin tattaunawa a kan dangantakarsu da ta yi rauni da kuma tattaunawa a kan bukatar hukumomi dake Kabul na tattaunawa da Taliban a zaman hanyar kawo karshen rikicin kasar.


Jami’ai a babban birnin Pakistan Islamabad sun ce Abbasi zai kai ziyarar wuni guda ne bisa gayyatar da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya bashi, a kan neman taimakon Pakistan, ta shiga tsakanin tattaunawa da Taliban.


Shugabannin biyu zasu kuma tattauna a kan kawo karshen tsamin dangantakarsu da kuma hanyoyin bunkasa dangantakar siyasa da tattalin arziki da tsaro da kuma yaki da ta’addanci.