Fursunoni Da Dama Sun Tsere Daga Gidan Yarin Comoros

Gidan yari

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ce fursunoni 38 ne suka tsere daga wani gidan yari mai cunkoso a Moroni, babban birnin kasar, bayan da wani soja da aka tsare ya fasa gidan yarin.

Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin kasar Comoros da ba shi da tsaro na kirki ta babbar kofar shiga.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ce fursunoni 38 ne suka tsere daga wani gidan yari mai cunkoso a Moroni, babban birnin kasar, bayan da wani soja da aka tsare ya fasa gidan yarin.

Gidan yari

Masu gabatar da kara sun ce fursunonin sun yi amfani da rashin tsaro mara inganci ne sannan suka fita ta babbar kofa. Babu wanda ya jikkata a lamarin.

Sun ce akwai yiyuwar wani soja ne ya shirya fasa gidan yarin, wanda aka kama shi kan mutuwar wani mai sha’awar kwallon kafa da jami’an tsaro suka bindige yayin da suke kokarin tare magoya bayan masu kwallo, kafin wasan shiga gasar cin kofin duniya a bara.

Sojan na cikin wadanda suka tsere, sai dai kawo yanzu ba a kama ko daya daga cikinsu ba.