GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Maris,1, 2018, Bibiya Kan Sace 'Yammatan Dapchi Kashi Na Daya

Grace Alheri Abdu

Ranar Litinin sha tara ga watan Fabrairu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai hari a makarantar sakandaren 'yammata dake garin Dapchi, cikin jihar Yobe, suka yi awon gaba da 'yammatan da kawo yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da sace dari da goma bayanda da farko aka musanta cewa sacesu aka yi. Wannan lamarin dai na faruwa ne bayan kimanin shekaru hudu da sace 'yammatan sakandaren Chibok dari biyu da sab'in da shida a wani lamari irin wannan. Abinda ya dauki hankalin shirin Domin Iyali ke nan wannan mako. Wakilinmu Haruna Dauda Bi'u ya sami zantawa da shugaban kungiyar iyayen da aka sace 'ya'yansu Mallam Bashir Manzo wanda ya fara da bayyana yadda wannan lamarin ya auku, yayinda gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya bayyana kokarin da jami'an tsaro ke yi na ceto 'yammatan. Saurari bayanansu da kuma wadansu hirarraki a shirin.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton sace 'yammatan Dapchi-10:30"