GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Maris,15, 2018, Hira da Yammata Da Suka Kubuta Daga Hannun Boko Haram: Kashi Na Daya

Grace Alheri Abdu

Makon jiya, aka gudanar da bukin ranar mata ta duniya, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin jawo hankalin al'umma kan matsaloli dake tauye rayuwar mata. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da mata musamman daruruwan 'yammata da kungiyar Boko Haram take garkuwa dasu, a arewa maso gabashin Najeriya, ke kara fuskantar kalubala da tauye hakkokinsu.

Bayan kammala bukin matan na duniya, Majalisar Dinkin Duniya kuma tana hada kan masu ruwa da tsaki daga dukan kasashen duniya, domin taron koli kan harkokin mata na makonni biyu, a shelkwatarta dake birnin New York. A bana, an jera sunayen manyan jami'an gwamnatocin kasashen duniya da cibiyoyi dari da saba'in da biyar da zasu gabatar da kasidu , a taron da taken “kalubalai da damar damawa da kowanne jinsi, da kuma inganta rayuwar matan karkara da kuma 'yammata.

Barrista Yakubu Saleh Bawa na daya daga cikin wadanda ke halartar taron, na kuma nemi sanin fa'idar gudanar da taron dab da kammala bukukuwan ranar mata ta duniya.

Shirin Domin Iyali ya kuma sami jin ta bakin wadansu daga cikin 'yammatan da kungiyar Boko Haram ta sace a garin Bama cikin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, wadanda suka ziyarci majalisar dokokin Amurka tare da tallafin wata cibiya mai zaman kanta ta Amurka wadda kuma ke daukar nauyin ilimantar dasu a Najeriya. Ga kadan daga cikin bayanin da daya daga cikinsu ta yi a wajen wani zaman tattaunawa da 'yammajalisar dokokin Amurka mata suka shirya. Ita dai wannan dalibar da zamu saya sunanta bisa dalilan tsaro,kungiyar Kungiyar Boko Haram ta sace ta ne tana da shekaru goma sha biyar, ta kuma yi mata auren dole.

Saurari cikakken shirin.

Your browser doesn’t support HTML5

Bama Boko Haram Victims/CWS-62-10:45"