Gwamnatin Jihar Neja Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Game Da Aikin Hako Mai A Yankin Bida

NEJA: GWMNAN JIHAR NEJA Alhaji Abubakar Sani Bello

Bayan da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya bada umarnin ci gaba da aikin neman Man fetur a yankin tafkin Chadi da ke Arewa maso Gabashin kasar. Al’ummar jihar Neja sun nuna bukatarsu na a nemo Man da aka Gano a yankin Bida.

Gwamnatin jihar Nejan ce ta fara fitar da wata sanarwa dake nuna bukatar gwamantin Najeriyar ta kula da aikin neman Man dake yankin nata.

Kwamishinan labarai na jihar Neja Mr. Jonathan Vatsa, ya yi kira ga shugaban kasa da cewa yadda yake kokarin ganin an hako mai a yankin tafkin Chadi, da ya taimaka a hada da na tafkin Bida domin a samu wadatar mai a Arewacin Najeriya.

Shima lauya mai zaman kansa a Najeriya Barista Bala Marka, ya nuna farin cikinsa ga umarnin shugaban kasa, na a nemo inda mai yake a tafkin Chadi. Ya kuma roki shugaban da ya bayar da umarni a nemi man da ke yankin Bida.

A baya dai tsohuwar gwamnatin Babangida Aliyu, ta gudanar da aikin binciko man a yankin Bida, inda bayanai suka nuna akwai man da ma wasu dinbin albarkatun kasa dake kwance a yankin.

Saurari rahotan Mustapha Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Neja Tayi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Game Da Aikin Hako Mai A Yankin Bida - 2'55"