Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kashe Boderi Isyaku, Dan-Fashin Dajin Da Ya Addabi Jihohin Arewa

Boderi Isyaku

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe Boderi Isyaku kasurgumin dan-fashin dajin nan da ya addabi jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara Naija da Abuja, tare da wasu manyan 'yan-bindigan dake tare da shi.

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da cewa Boderi Isyaku ne da ya jagoranci manyan hare-hare a jihar Kaduna da ma wasu makwabtan jahohi, inji mukaddashin kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, malam Samuel Aruwan.

Masana harkokin tsaro irin su manjo Yahaya shinko mai-ritaya na ganin dole a jinjinawa jami'an tsaro kan wannan kokari amma ya ce wajibi su cigaba ta tashi tsaye.

A hirar shi da Muryar Amurka, Alh. Dayyabu Kerawa wanda ya jagoranci al-umar garurrruwan da ke yammacin Zariya da su ka yi koke a kan yadda 'yan-bindiga ke kai hare-hare a yankunan su, kuma ya ce jin labarin kashe kasurgumin dan-fashin dajin ya sa sun fara ji akwai yuwuwar su koma noma bana.

Cikin watan Fabarairun nan dai 'yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu yankunan kananan hukumomin Igabi, Giwa, Chukun, Kaura da Kajuru sai dai ana sa ran wannan nasarar kashe 'yan-fashin dajin, ka iya kawo karshen barazanar tsaro a wadan nan yankuna.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Kashe Kasurgumin Dan-Fashin Dajin Da Ya Addabi Jahohin Arewa, Boderi Isyaku