Har Yanzu Babu Alamar Karshen Matsalar Karancin Man Fetur

Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a birnin Lagos, bayan da aka cire tallafin mai.

Duk da ikirarin kamfanin man fetur cewa an samar da man fetur mai yawa a Lagos, har yanzu ana karancinsa sosai cikin jihar da dukkan makwabtanta
Har yanzu ananci gaba da fama da mummunar matsalar karancin man fetur a cikin Lagos da jihohi makwabtanta, duk kuwa da ikirarin da kamfanin man fetur na Najeriya yayi cewa an samar da mai da yawa a nan Lagos.

Wakilin Sashen Hausa, Ladan Ibrahim Ayawa, yace kusan dukkan gidajen man da ya ziyarta su na kulle a jumma'ar nan.

Sale Bello dake zaune a Unguwar Ijanike a hanyar Badagry, yace ana sayarda litar mai daya a kan Naira 150 a inda yake, maimakon Naira 97.

Shi ma Sarkin Kanuri na Lagos, Mai Sale Mustapha, yace babu mai a gidajen man dake nan, sai a kasuwannin bayan fage ake samu.

Wannan labarin haka yake a jihohi makwabtan Lagos. Dele Ayodu na gidan rediyon Rock City FM a Abeokuta, ya fadawa wakilin Sashen Hausa cewa babu mai a hedkwatar ta jihar Ogun.

Daga Ibadan ma, wakilin Sashen Hausa, Hassan Umar Tambuwal, yace ana karancin man sosai a Jihar Oyo. Haka wannan labarin yake a dukkan jihohin dake kudu maso yammaci.

A arewacin Najeriya ma, ana ci gaba da fama da wannan matsala ta karancin man fetur.

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Karancin Fetur na Kara Yin Tsanani - 2'32"