KANO: Harkokin Sufuri Na Fuskantar Kalubale Sanadiyar Yajin Aiki Adaidaita Sahu

Kungiyar masu sana’ar tuka babur mai kafa uku

Batun biyan harajin naira 100 ga gwamnati kuma a dunkule na tsawon shekara guda shine musabbabin takaddamar da ta kaure tsakanin matuka adai-daita sahun da kuma hukumar KARATO mai kula da zirga zirgar ababen hawa wadda tun a makon jiya aka fara kai ruwa rana tsakanin jami’anta da matuka baburan mai kafa uku.

Yajin aikin yan Adaidaita sahu Kano

Wannan lamari dai ya kawo cikas ga zirga zirgar Jama’a a birnin da kewayen Kano a yau litinin musamman ga ma’aikata, dalibai da kuma ‘yan kasuwa.

Ya zuwa yanzu dai Uwar kungiyar matuka baburan na adai-daita sahu a Kano ta nesanta kanta da wannan yajin aiki da ‘yayan ta keyi.

Ga alama wannan takaddama ta sanya hukumar KAROTA mai kula da zirga zirgar Ababen hawa a Kano baiwa gwamnatin shawarar rusa tsarin sufurin adai-daita sahu a jihar Kano, kamar yadda shugabanta Babbafa Babba DanAgundi ya tabbatar.

Yajin aikin yan Adaidaita sahu Kano

Gwamnatin Kano ta Malam Ibrahim Shekarau ce ta bullo da tsarin sufuri na adai-daita sahu kuma Dr Saidu Ahamad Dukawa na cikin wadanda suka bada gudunmawar samar da tsarin a wancan lokaci.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KANO: Harkokin Sufuri A Kano Na Fuskantar Kalubale Sanadiyar Yajin Aiki Masu Adaidaita Sahu