Hukumar NEMA Ta Fara Kai wa Wadanda Rikicin Numan Ya Shafa Agaji

Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, NEMA, ta fara kai kayayyakin tallafi ga wadanda rikicin makiyaya da 'yan Bachama ya shafa a jihar Adamawa.

Kamar yadda alkalumma ke nunawa, daruruwan mutane ne rikicin ya raba da gidajensu a kananan hukumomin Demsa da kuma Numan da ke kudancin jihar Adamawa

Rahotannin sun ce yanzu hukumar NEMA, fara kai kayayyakin tallafi ga mutanen yankin.

Sabon jami’in hukumar NEMA mai kula da shiyyar Yola, Imam Abani Garki, ya ce hukumar za ta ci gaba da ba da gudunmuwarta.

Shugabar karamar hukumar Demsa Mrs. Wale Fwa, ta yaba da samun kayan, inda ta ce tuni ma suka kafa kwamitin da zai raba kayan.

Babban sakataren hukumar ADSEMA mai ba da agajin gaggawa a matakin jiha, Mallam Haruna Hamman Furo ya ce bisa tsarin da ya gani ya yi imanin cewa wadanda lamarin ya shafa za su amfana.

Wasu daga cikin wadanda rikicin ya shafa sun bayyana farin cikinsu game da tallafin.

Domin karin bayani ga cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar NEMA Ta Fara Kai wa Wadanda Rikicin Numan Ya Shafa Agaji - 3'04"