Hukumar Zaben Najeriya Ta Ce Ba Zata Bada Sakamakon Wucin-Gadi Ba

Shugaban hukumar Zabe ta Najeriya, INEC, Farfesa Attahiru Jega

Haka kuma hukumar ta ce ba zata sake gudanar da zaben na gwamna a duk fadin Jihar Anambra ba sai a wuraren da aka samu matsala kawai
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ba zata bayyana wani sakakon wucin-gadi game da zaben gwamnan Jihar Anambra ba har sai bayan an gudanar da zaben a wuraren da aka samu matsala cikin wata karamar hukumar guda a jihar.

Ya zuwa yanzu dai, sakamakon kananan hukumomi guda 19 daga cikin 20 na jihar aka bayyana, a saboda matsalolin da suka shafi magudi da aka gano a karamar hukumar guda inda mutane dubu 113 ba su samu damar jefa kuri'a ba, ko kuma sun jefa an sace.

Wata kwamishinar zabe a huku mar ta INEC, Hajiya Amina Zakari, ta yi watsi da kiran da wasu sassa keyi na cewa a soke zaben baki dayansa a sake gudanar da sabo a duk fadin jihar, tana mai fadin cewa neman kuntatawa mutanen da suka jefa kuri'unsu kuma aka kidaya a kananan hukumomi 19 ne a ce su sake komawa don an samu wata matsala a wata karamar hukumar da ba ta su ba.

Haka kuma, ta ce neman a sake gudanar da zabe a duk fadin jihar ta Anambra, bayarda dama ne ga wadanda suka nemi yin magudi a ranar zaben su sake neman dama lissafin wannan zabe in sun ga ba zasu iya lashewa ba.

Ta ce tilas ne a yi ma dukkan 'yan takara adalci ta hanyar dakatar da bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Anambra har sai bayan an jefa dukkan kuri'u, kuma an kidaya su, ganin cewa yawan kuri'un da ba a kada ba, sun zarce ratar dake tsakanin wadannan 'yan takara a yanzu.

Har yanzu dai hukumar ta INEC ba ta saka takamammiyar ranar gudanar da zaben a wannan karamar hukuma da aka soke ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar INEC Kan Zaben Jihar Anambra - 3'58"