Accessibility links

Ana Shirin Zaben Gwamnan Jihar Anambara Gobe Asabar. 'Yan Takara 23 Ne su ka Tsaya

  • Ibrahim Garba

Gwamna Peter Obi na jihar Anambara

Ana nan ana ta shirin gudanar da zaben Gwamnan jihar Anambara a gobe Asabar.

Idon duniya na kan jihar Anambara ta kudu maso gabashin Nijeriya, inda za a gudanar da zaben Gwamna a gobe Asabar bayan kammala wa’adin shekaru 8 da Gwamna Peter Obi na jihar ya yi.

Wakilinmu na yankin Naija Delta Lamido Abubakar, wanda a yanzu haka ya ke garin Awka, hedikwatar jihar Anambarar, ya ce ga dukkan alamu kuma bisa yadda ya ke ji daga jama’a an shirya sosai, a yayin da jami’an tsaro kuma ke girke a muhimman wuraren jihar ciki har da wuraren duba ababen hawa. Lamido ya ce ‘yan takara 23 ne a zaben na gwamna.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Shiyyar Jihar Anambra, Mr Franc Mbo ya gaya ma Lamido cewa sun kammala raba kayan zabe a dukkannin kananan hukumomi 21 da ke jihar. Haka zalika, wani mazaunin garin na Anambra mai suna Ifanyi Opara ya gaya ma Lamido cewa shi ma ya shaida cewa an yi shiri sosai. Shi kuwa Chief Stephen Okochukwu kira ya yi ga shugaban Hukumar Zaben Furfesa Attahiru Jega da ya dubi Allah ya tabbatar cewa an yi dukkan abin da ya dace a zaben saboda cigaban Nijeriya baki daya.

Wakilin namu y ace Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Alhaji Bello Nasarawa ya gaya masa cewa an samar da jami’an tsaro wajen dubu goma don ganin an yi komai cikin kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG