Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin PDP-Sabuwa Zasu Gaji Su Komo - In Ji Tafidan Bodinga Abubakar Aliyu


Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja
Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja

Shi kuma Hussaini Gariko, dan NEPU-Sawaba, cewa yayi ya kamata gwamnonin su zamewa PDP-Tsohuwa kadangaren bakin tulu

Sarkin yakin tazarcen shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, Abubakar Aliyu, Tafidan Bodinga, yace gwamnaonin nan da suke yi ma jam'iyyar tawaye, suka ware suka kafa PDP-Sabuwa, zasu gaji da wannan tayar da kayar bayan, su kuma komo cikin uwar jam'iyyar.

Har yanzu, babu wata alamar dake nuna cewa 'yan PDP-Sabuwar zasu ci gaba da zama a PDP ne ko kuma zasu karbi goron gahyyatar shiga wata jam'iyyar dabam.

Tafidan na Bodinga, yace akwai takaici ganin cewa wasu jam'iyyu su na can su na ta yakin neman zabe yayin da su a PDP suke ta fada. Yace shugaban PDP-Tsohuwa, Bamanga Tukur, mutum ne wanda a dalilin hakurinsa jam'iyyar ta kai matsayin da take.

Sai dai kuma wani dan NEPU-Sawaba, Hussaini Gariko, ya shawarci gwamnonin dake tawayen da su ci gaba da zamewa jam'iyyar PDP-Tsohuwa kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu, a kyale ka, ka bata ruwa.

Yace muddin ba a biya musu bukatunsu ba, to sake hadewa da PDP-Tsohuwa babban hatsari ne ga wadanda suke yin tawayen.

Ga cikakken bayani a bakin Nasiru Adamu el-Hikaya.

Gardamar PDP-Sabuwa da PDP-Tsohuwa - 2:53
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG