ISIS Sun Yabi Balaraben Bafaranshen Da Ya Hallaka Mutane 84 da Jikkata 200

Mohamed Lahouaiej Bouhlel, Matukin Babbar Motar Da Ta Ya Kutsa Cikin Dandazon Jama a Birnin Nice

A yau Asabar kasar Faransa ta fara hutun zaman makokin da ta bayar a duk fadin kasar na mummunan harin nan da aka kai da babbar motar ya kashe mutane 84 hade da yara 10, guda 200 kuma suka jikkata.

Wani Bafaranshen balarabe dan asalin kasar Tunusia Mohamed Lahouaiej Bouhlel mai shekaru 31 ne kuma mazaunin garin na Nice ya kutsa da gwangwaron cikin al’ummar a shekaran jiya.

A lokacin da jama’a ke bikin ‘yanci da bwalwala da ake kira Bastille Day a birnin Nice na kasar. Rahotannin sunce hukumomi basu kalleshi a dan’tadda a baya, duk da cewa ansha kamashi da ‘yan kananan laifuffuka.

Daga cikin laifuffukansa har da wani rikici da makamin da aka yi a watan Janairu, wanda hakan ya ja masa daurin talala na gyara halinka na wata 6.

Tsohuwar matar Mohamed din da har suna da ‘ya’ya 3 da ita, tana cikin wadanda ‘yan sanda ke wa tambayoyi akansa don gano ko yana da alaka da ‘yan ta’adda irin su ISIS, musamman ma da a yau suka bayyana Bouhlel a matsayin sojansu.