Iyayen Daliban Cibok na Fama da Bakin Ciki

  • Ibrahim Garba

Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna maida jawabi a taron da suka yi da gwamna jihar Borno, a Chibok, jihar Borno, 22 Afrilu 2014.

Kowace ranar Allah takaicin iyayen dalibai matan da aka sace a Chibok sai karuwa ya ke yi saboda rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki da kuma jita-jita daban-daban da su ke ta ji.
Daya daga cikin iyayen dalibai matan da aka sace a wata makaranta a Chibok da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce su iyayen 'yan matan da aka sace na cikin matukar takaici da bakin ciki saboda fargabar irin yanayin da yaran za su sami kansu a ciki da kuma jita-jita da rashin samun bayanai daga hukumomin tsaro.

Da ya ke bayani ma abokin aikinmu Bello Habib Galadanchi, daya daga cikin iyayen 'yan matan ya ce a baya-bayan nan sun ji cewa an ga 'yan matan a wajejen Monguno da Marte da Kukawa da dai sauransu. Ya ce a baya an gaya masu cewa 'yan matan na dajin Sambisa har wasu iyayen su ka je wurin sai kuma gashi su na jin jita-jita iri-iri. Ya ce har yanzu iyaye dai na kai kukansu wurin gwamnati. Kuma akwai wajen 'yan mata 193 a hannun 'yan bindigar.

Ya ce kwanan baya an gaya masu cewa 'yan bindigar na shirin wucewa da 'yan matan zuwa wani wuri a jihar Adamawa don haka su ka fito da matasan garin su ka tare hanya amma ba su ga kowa ba. Ya ce gashi yanzu kuma ana ce masu ana jin duriyar 'yan matan a wajejen Monguno da Marte da sauransu. Ya ce wannan al'amari ya jefa su cikin matsanaciyar damuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Daga Cikin Iyayen 'Yan Matan da Aka Sace - 3'35"