Jakadan Rasha Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani a Amurka

Dadadden Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vitaly Churkin, ya mutu ba zato ba tsammani jiya Litini a birnin New York, kwana guda kafin ya cika shekaru 65 da haihuwa.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayar da sanarwar rasuwar tasa a wata takardar bayani, ba tare da bayyana musabbabin rusuwar ba. Shugaban babban zauren MDD Peter Thomson ya gaya ma Muryar Amurka cewa an gaya masa cewa Churkin ya gamu ne da bugun zuciya a ofishin jakadancin Rasha, aka kai shi asibiti, inda ya mutu.

Nan da nan takwarorin aikinsa na diflomasiyya su ka shiga shafukansu na sada zumunci su ka yi ta bayyana alhininsu da juyayinsu kan mutuwarsa ta ba zata.

"Na yi matukar bakin ciki da jin cewa aboki na kuma takwaran aiki na Vitaly Churkin ya mutu," a cewar jami'in diflomasiyyar Burtaniya a MDD Matthew Rycroft, wanda ya kara da cewa "Allah ya jikan shahararren jami'in diflomasiyya kuma gwarzo."