Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Ta Da Niyar Kwace Man Kasar Iraqi


Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis ya fadi jiya Litini cewa, Amurka ba ta da niyyar kwace man kasar Iraki, wani abin da a baya shugaba Trump ya ba da shawarar a yi, a matsayin ganimar yakin da sojojin Amurka ke yi a can, kuma saboda a hana kungiyar ISIS samu ta sayar.

Mattis ya yi hira da manema labaran da su ka bi shi zuwa Iraki a wata ziyarar ba zata, wadda ta zo a rana ta biyu ta farmakin sojin da aka kaddamar na yinkurin korar ISIS daga sashin Yamma na birnin Mosul.

"Ina tsammanin dai dukkanmu da ke wannan dakin, dukkanmu da ke Amurka, da kanmu mu ke sayen man fetur da kuma iskar gas, kuma na tabbata za mu cigaba da yin haka," a cewar Mattis, wanda ya kara da cewa, "Ba mun zo Irak ne don mu kwace man wani ba."

Mattis ya kuma sha alwashin goyon bayan Iraki a tsawon yakin da ta ke yi da ISIS. "Ina mai ba ku tabbacin cewa za mu cigaba da goyon bayanku a tsawon wannan yakin. Za mu kasance tare da ku da kuma sojojinku har zuwa nan gaba, ta yadda sojojin Iraki ne kadai, ba wasu ba, za su rinka kare diyaucin kasar," a cewarsa.

Da aka tambaye shi ko Amurka za ta cigaba da zama a Iraki bayan yakin Mosul, sai ya ce, "Ina ganin za mu dade mu na wannan yakin, kuma za mu cigaba da goyon bayan juna."

Laftana-Janar Stephen Townsend, wanda ya jagoranci rundunar gamayyar da Amurka ke jagoranta, wadda ke kokarin fatattakar ISIS, shi kuma har cewa ya yi, "Ba na jin gwamnatin Iraki za ta bukaci mu fice nan da nan bayan yakin Mosul. Ina ganin gwamnatin Iraki ta fahimci cewa wannan yaki ne mai daure kai, kuma za ta bukaci sojojin gamayya ko ma bayan yakin Mosul."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG