Jam'iyar APC Ta Kaddamar Da Kwamitin Sulhu Na Kasa

Membobin kwamitin sasantawa na jam'iyar APC

A hirarsa da Muryar Amurka, shugaban kwamitin rikon kwarya na Jamiyyar Mai Mala Buni ya bayyana cewa,an kafa kwamitin ne domin sasanta mambobin da suka fusata sakamakon za6ukan da aka gudanar a kasar.

shugaban kwamitin rikon ya kaddamar da komitin mutum 9, a karkashin jagorancin dan majalisar Dattawa mai wakiltan jihar Nasarawa ta Yamma Abdullahi Adamu,

Membobin kwamitin sasantawa na jam'iyar APC

Buni ya ce dama akwai korafe korafe daga 'ya'yan jamiyyar daga shiyoyi daban daban na kasar, saboda haka kafa wanan kwamitin hanya ce ta magance su.

A lokacin da yake bayanin matakan da komitin zai dauka wajen yin sulhu musamman ma hada kan 'ya'yan Jamiyyar Shugaban Komitin Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, suna da kwarin guiwa rikicin cikin gida da jam'iyar ke fuskanta a halin yanzu ba zai sa ta sami koma baya a zabuka na gaba ba.

Sauran mambobin komitin su ne tsoffin gwamnoni guda uku, da George Akume na Jihar Binuwai, da Sulivan Chime na Jihar Enugu da Ali Sa'ad Birnin kudu na Jigawa, da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara sai Sakataren Komitin Moses Adeyemo.

pdp-ta-amince-da-mika-shugabancin-jam-iyyar-ga-yankin-arewa

abin-da-masana-ke-cewa-kan-zaben-shugabanni-da-apc-ta-yi-a-kananan-hukumomi

za-mu-gudanar-da-tarukan-zaben-shugabanni-duk-da-umarnin-kotu---apc

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

APC ta kaddamar da kwamitin sasantawa:3:00"