Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Amince Da Mika Shugabancin Jam’iyyar Ga Yankin Arewa


Zauren taron da jam'iyyar PDP ta yi A Abuja (Facebook/PDP)
Zauren taron da jam'iyyar PDP ta yi A Abuja (Facebook/PDP)

Sakataren jam’iyyar na kasa Mr. Kola Ologbondiyan ne ya fadawa manema labarai wannan matsaya da aka cimma bayan taron kwamitin zartawar jam’iyyar na kasa da aka yi a Abuja a ranar Alhamis.

Babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya, ta tabbatar da mika mukamin shugaban jam’iyyar ga yankin arewacin kasar.

A kwanakin baya, kwamitin da jam'iyyar ta kafa don duba batun raba mukamai a tsakanin shiyyoyin kasar, ya ba da shawarar a ba arewacin kasar mukamin shugabancin jam’iyyar.

Sakataren jam’iyyar na kasa Mr. Kola Ologbondiyan ne ya fadawa manema labarai wannan matsaya da aka cimma bayan taron kwamitin zartawar jam’iyyar na kasa da aka yi a Abuja a ranar Alhamis inda jam'iyyar ta karbi wannan shawara.

Bisa wannan matsaya, dukkan mukaman da kudancin kasar suke rike da su a jam’iyyar za su koma arewa sannan na arewa su koma kudu.

Wasu masu hasashen sun yi hangen cewa bisa wannan tsari, dan takarar mukamin shugaban kasa daga jam’iyyar zai fito ne daga kudanci tun da an ba arewa mukamin shugabancin jam’iyyar, domin tsarin da jam’iyyar take bi kenan.

Wato idan shugaban jam’iyyar ya fito daga wani yanki sai a ba wani yanki tikitin takarar shugaban kasa.

Rahotanni sun ruwaito tsohon matamaikin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya halarci taron yana cewa, batun mulkin karba-karba ba shi ne mafita ga matsalolin Najeriya ba.

Ya kara da cewa shugaban kasar zai iya fitowa daga ko ina a yankunan kasar yayin da jam’iyyar ta PDP ke kokarin karbar mulki daga hannun APC.

Rahotanni sun yi nuni da cewa tuni Atiku ya fara shirye-shiryen tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar ta PDP.

A ranakun 30-31 ga watan Oktoban, jam’iyyar ta shirya gudanar da babban taronta.

XS
SM
MD
LG