Jirgin Farko Ya Tashi Ran Asabar Da Alhazai 500

Jirgin alhazan Najeriya na farko zuwa Saudiyya

Alhazan Najeriya sun fara tafiya aikin Hajji a kasar Saudiyya
Wakillin Sashen Hausa na shiyar Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu ya aiko ma na da rahoton cewa rukunin alhazan Najeriya na farko kimanin dari biyar ya tashi da la'asariyar asabar daga babban filin jirgin saman Maiduguri, jahar Borno. Manyan jami'an da suka halarci kaddamar da tashin jirgin saman na Max Air sun hada da mataimakin shugaban kasar Najeriya Arch. Mohammed Namadi Sambo da gwamnonin Borno da Yobe da Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar na uku da kuma Shehun Borno wanda shi ne Amirul Hajjin bana. Mataimakin shugaban kasar Najeriya Arch. Mohammed Namadi Sambo ne ya fara yin jawabi kamar haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin farko ya tashi da alhazai 500 daga Borno.-2':30"