Jirgin Kasa Yayi Hadari a Legas

Hadarin jirgin kasa.

Wani jirgin kasa da ya taso daga Kano ya samu hadari a Legas sanadiyar rashin birki
Jirgin kasan da ya taso daga Kano ya samu hadari a Legas wanda yayi sanadiyar asarar rayuka.

Mutane sama da saba'in ne ke kwance a asibiti domin raunuka da suka samu sanadiyar hadarin jirgin kasan da ya taso daga Kano. Wasu tara kuma sun mutu nan take.

Direban karshe mai suna Shakiru ya karbi tukin jirgin ne a garin Ibadan. Amma tun daga garin Abeokuta ya samu matsalar birki har ya isa birnin Legas a guje. Direban na cikin wadanda suka rasu. Mataimakin direban ma ba'a samu a fitar da gawarsa ba wadda ta rabu da kansa.

Hukumar jirgin kasan ta kasa ta hana kowa shiga inda jirgin yake. Sakamakon rashin birki yasa jirgin ya zarce inda yakamata ya tsaya lamarin da yasa jirgin ya banke mutane dake kan hanya.

To amma masana aikin jirgin kasa sun ce idan an samu matsalar birki wani da ake kira gadman dake can baya na iya tsayar da jirgin ya hanashi tafiya. Wasu sun ce kawo wadanda ba kwararru ba ne akan aikin jirgin kasa su yi aikin yake haddasa irin hadarin da ya faru. Misali wanda aka sa a matsayin daraktan zirga-zirgan jiragen kasa bai san kan aikin ba amma aka kawoshi aka dorashi bisa mukamin.

Ga rahoton Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin Kasa Yayi Hadari a Legas - 2'30"