Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Asabar Ake sa Ran Za'a Yi Jana'izar Marigayi Sarki Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta


Marigayi sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta da 'Yan Boko Haram suka kashe.

Sarkin wanda Allah Ya yiwa cikawa sakamakon kwanton bauna da 'yan binidga na Boko Harama suka yi musu suna kan hanyar zuwa jan'izar sarkin Gombe ne.

A Yau Asabar ake sa ran za a yi jana’izar mai martaba sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idris Timta, wanda Allah Ya yiwa rasuwa sakamakon wani kwanton bauna da ‘yan binidga da ake jin ‘yan Boko Haram suka yiwa jerin gwanon motocin sarakunan, a wani daji tsakanin Zur da shafa cikin karamar hukumar Hawul cikin jihar Borno ranar jumma’a.

Sarakunan suna kan hanyarsu ne zuwa Gombe domin su halarci jana'izar sarkin Gomben Alhaji Abubakar Umar, wanda Allah Ya yiwa cikawa a wani asibiti a Landan baya ya juma yana jinya.

Ga Karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG