Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sandan Najeriya Ya Fasa Kwai - Kashi na Uku


Cin hanci yayiwa shugabannin yansandan Najeriya katutu inda suke danne kowane taimako aka bayar saidai na iyalan wadanda suka mutu domin gwamnan jihar Borno yana tabbatar kudin an baiwa wadanda abun ya shafa.

Babu kudin da shugabannin 'yansanda ba zasu danne ba sai wanda ya zama dole domin an fallasawa duniya. Shi ne kadai ba zasu taba ba. Duk wani abun da yakamata a ba na kasa zasu danne. Sai dai a ce Allah Ya isa.

Cin zalunci yayi nisa sai dai a barwa Allah. Ko shugaban su bari ko kuma Allah Ya hukuntasu watarana nan gaba.

Dangane da ko menene Mopol Malu yake son jama'a masu sauraro su yi sai yace "ina roko da babbar murya su taimaka mana" Yana son su dauki wani matakin gaggawa da zasu gyara yanayin aikin 'yansanda a kasar. Su bi wadanda ke bakin daga su bincika su ji abubuwan dake faruwa. Kada su tambayi na ofis. Jama'a su tambayi 'yansanda daga kurata har zuwa mai matsayin sifeto domin su samu gaskiya. Duk wadanda suka wuce wannan matsayin sun zama daya daga cikinsu. Tare ake hada baki a ci zaluncinsu. Da sun hau sama sun manta da zalunci da suka sha domin su ma sun shiga kungiyar cin zalunci da azzalumai

Yace suna ja baya domin duk wanda ya rasa ransa ya zama abun wulakanci. Babu wanda zai kula da shi. Dole su ja baya. Aikin ba kayan gado ba ne. Kayan aiki ba abun da zasu kwasa ba ne da kansu ba. Idan kuma ka kashe mutum su sa maka ankwa a hannu su ce ka yi kashin kai domin su manyan babu 'ya'yansu a kasan sabili da haka suna yin abun da suka ga dama. Suna cin karensu ba babbaka.

Shi Mopol Malu yana kiran jama'a su taimaka. Sun shiga aikin dansanda ne su taimaki kasarsu amma yanzu sun zama abun cinkasuwa da su. Yace tun da ya tashi ruwa kawai ya wanke baki dashi bai ci komi ba domin bashi da kudin cin abincin. Inda da suke cin abinci an koresu an ce kada su basu abincin. Su kan ci bashi idan an biyasu kudin wata su biya domin basu da wani alawus. Sai dai ka cinye albashinka idan har an biyan. 'Ya'ya kuma da iyalai suna gida suna kukan yunwa. Matan da suke sayar masu da abinci a cikin barikinsu an hanasu. Matan ba daga waje suke zuwa ba. Matan yansanda ne. Su ne suke basu bashi idan an biyasu su biya matan. Yanzu da aka hana basu san inda zasu ba.

Mopol Malu ya kira wadanda ke kan kujera su ji tsoron Allah. Idan basu tuba ba hukuncin Allah na zuwa kansu.

Shikenan hirar da Muryar Amurka yayi da dan Sanda. A labaran baya mun kawo muku martanin da jami'an suka bayar, suka ce dama akwai wannan matsalar cin hanci da danniya tun da dadewa, sannan yanzu kuma wannan matsala tayi musu bazata.
XS
SM
MD
LG