Shirin Kasuwa na wannan makon ya leka kasuwar AYA da ke kusa da fadar shugaban Najeriya a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya don jin yadda ake hada-hadar kasuwanci.
WASHINGTON, DC - Wakilin Murya Amurka Nasiru Adamu Elhikya ya zagaya kasuwar AYA inda ya yi hira da 'yan kasuwa da suka bayyana masa farashin kayayyaki.
A wannan kasuwa dai ana saida abubuwa da yawa kama daga abinci, magunguna, kayan kwalliya da sauran kayayyakin masarufi.
A daidai lokacin da al'umar musulmi ke azumin watan Ramadan, 'yan kasuwar sun ce harkar kasuwancin yanzu ba kamar da bane.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5
Kasuwar AYA a Birnin Tarayya Abuja