Kotun ICC Ta Baiwa Tsohon Shugaban Hukumar Tsaron Libya Sammaci

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a jiya Litinin ta bada takardan sammacin kama tsohon shugaban hukumar tsaron Lybia bisa zarginsa da aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil adama a yunkurin kawar da yan adawan tsohon shugaban kama karya Moammar Gadhafi.

Sammacin farko da kotun ta bayar a shekarar 2013, yana tuhumar Al-Tuhamy Mohamed Khaleed da aikata laifuka guda uku na yaki da wasu Karin laifuka hudu na cin zarafin bil adama.

Sammacin da aka bayar a kan Al-Tuhamy na cewar tsakanin watan Faburairu da Agusta na shekarar 2011 ma’aikatar soji da hukumomin tattara bayanan sirri da na tsaro, sun kai hare hare a kan fararen hula a wani matakin gudanar da wani tsarin da zai kawar da jami’iyar da take adawa ga mulkin Gadhafi ta kowane hali.

Wadannan matakai sun hada da kisa da kame da tsarewa tare da azabtarwa da kuma cin zarafin wadanda ake musu kallon yan adawa.

A matsayinsa na shugaban hukumar tsaro, Al-Tuhamy shine ke da hurumin aiwatar da umarnin shugaba Gadhafi a cewar sammacin.