Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Tsaron Amurka Ya Ziyarci Kasar Djibouti


Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis ya ziyarci Djibouti, 'yar karamar kasar na ta arewa maso gabashin Afirka inda nan ne kadai Amurka ke da sojoji a Nahiyar Afirka, a ziyarce-ziyarcen gabas ta tsakiya da kuryar Afirka da ya ke yi.

Mattis ya kira Djibouti, wadda ke daura da mashigar ruwan Bab el-Mandeb, da 'wata muhimmiyar magama.' Jiragen yaki da dama kan bi ta wannan mashigar kulluyaumin, sannan kuma sojojin ruwan Amurka da Faransa da kuma wasu kasashen wajen 10 na amfani da tashar jirgin ruwan Djibouti dinnan mai zurfi, a cewar wani jami'in Amurka.

Baya ga jawabin da ya yi ga sojojin Amurka da na Faransa a Sansanin Lemonnier jiya Lahadi, Mattis ya gana da Shugaban Djibouti da kuma Ministan Tsaro.

Wannan tashar ta na da matukar muhimmanci ga atisaye da sauran harkokin da Amurka kan yi a Nahiyar Amurka, kuma sojojin Amurka na musamman na amfani da tashar wajen dakile harkokin ta'addancin kungiyar al-Shabab da ke makwabciyar kasa ta Somaliya, a cewar jami'ai.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG