Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Fashewa Ta Hallaka Sojojin Somaliya 9


Dakarun Somalia

Sojojin Somaliya 9 sun halaka sannan wasu biyar kuma sun samu raunuka, a wata babbar fashewa ta gefen hanya, wadda aka auna kan motar sojojin a Galgala, a cewar jami'ai.

Wannan fashewar ta auku ne da safiyar jiya Lahadi, yayin da jami'an tsaron Puntland ke gudanar da wasu harkokin tsaro akan tsaunin Galgala.

Mai magana da yawun 'yan sandan Puntland da ke Galgala, Manjo Abdurrahman Farah Gurhan, ya gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa motar na jigilar sojoji 17 bayin da bam, hadin gida din, ya tashi da su. Inda abin ya faru na da tazarar kilomita 57 kudu maso yammacin garin Bosso mai tashar jirgin ruwa.

"Sojoji 9 ne su ka mutu, wasu biyar kuma su ka ji raunuka, su na tafiya ne cikin wata mota yayin da bam din ya tarwatse," a cewar Gurhan.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG