Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala shugabar WTO.

Kungiyar Cinikayya ta Duniya ta fitar da wani faifan bidiyo da nufin gabatar da sabuwar shugabar da aka zaba yau.

Kungiyar ta wallafa faifan bidiyon ne jim kadan bayan sanar da zaben Ngozi Okonjo-Iweala mace ta farko kuma bakar fata ta farko da za ta jagoranci Kungiyar a tarihinta.

Zaben Shugabar WTO

A wani faifan bidiyo da Kungiyar WTO ta tallafa a shafinta na twitter ta nuna sabuwar shugabar kungiyar Ngozi Okonjo-Iweala a wani faifan bidiyo na tsawon minti daya da sakan hamsin jim kadan bayan sanar da zabenta.

Bidiyon ya hada da hirarraki da aka yi da ita da kuma bayanai da ta yi lokacin da take yakin neman zabe.

Tuni bidiyon ya fara daukar hankalin jama'a inda ake ta kallo da kuma yayatawa.

Kalli bidiyon

takarar-ngozi-okonjo-iweala-buhari-zai-shiga-kamfe

ecowas-ta-mara-wa-okonjo-iweala-baya

wace-ce-za-ta-zama-shugabar-wto-tsakanin-ngozi-okonjo-iweala-da-yoo-myung-hee

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.