Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wace Ce Za Ta Zama Shugabar WTO Tsakanin Ngozi Okonjo-Iweala Da Yoo Myung-hee?


FILE PHOTO: A sign is pictured in front of the chair of the Director General before the start of the General Council of the World Trade Organization (WTO) in Geneva

A karon farko, mace za ta jagoranci Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO bayan da aka kai mataki na karshe wanda babu namiji ko daya cikin 'yan takarar.

Hukumar Kasuwanci ta Duniya ta ce daga cikin mutum biyar da ke neman kujerar shugabancin hukumar an tsame mutum biyu kuma dukkansu mata ne.

Tsohuwar Ministar kudi a Najeriya, Okonjo-Iweala, za ta kara da ministar harkokin kasuwancin kasar Korea ta Kudu Yoo Myung-hee a wannan zagaye na karshe.

Hakan na nufin duk wanda aka zaba a cikinsu za ta zamanto mace ta farko da za ta shugabanci hukumar mai mambobi 164 a Geneva kamar yadda kakakin hukumar Keith Rockwell, ya bayyana.

Hakazalika duk wanda ya yi nasara a cikinsu, zai maye gurbin Roberto Azevedo dan kasar Brazil, wanda ya ajiye mukaminsa tun gabanin wa'adinsa ya kare.

Bayan da hukumar harkokin kasuwanci ta duniya WTO ta tabbatar da cewa Okonjo-Iweala mai shekara 66 ta samu nasarar kai wa wannan zagaye na karshe, ‘yan Najeriya da dama sun yi ta tsokaci kan wannan nasara.

Ministar ayyukan mata ta Najeriya, Pauline Tallen ta bayyana farin cikinta da matakin da Ngozi ta kai tana mai fadin cewa ba ta da shakka za ta samu wannan kujerar, saboda Allah ya ba matan Najeriya baiwa.

Fitacciyar ‘yar kasuwa a fannin kayata cikin gida, Laylah Ali Othman, ta bayyana jin dadinta game da wannan gagarumar nasara.

Shi ma dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba a jihar Gombe, Hon. Yunusa Abubakar Ahmad, ya taya Ngozi murna ya na mai cewa ba karamar martaba hakan ya janyo wa Najeriya da ma nahiyar Afrika ba, yana mai cewa, "‘yan Najeriya na alfahari da ita."

Ngozi Okonjo-Iweala, wadda aka haifa a garin Ogwashi Ukwu na karamar hukumar Aniocha ta kudu a jihar Delta, masaniyar harkar tattalin arziki ce daga Najeriya.

Ta kuma kawo sauye-sauye da yawa yayin da ta rike mukamin ministar kudi da jagorar tattalin arzikin Najeriya sau biyu kuma ta yi aiki a babban bankin duniya tsawon shekara 25.

A halin yanzu, ita ce shugabar cibiyar samar da rigakafi ta duniya.

Yoo Myung-hee mai shekara 53, ita ce ministar harkokin kasuwancin Korea ta Kudu, ta kasance mace ta farko da ta fara rike wannan mukamin a kasar.

Ana mata kallon kwararriya a harkokin kasuwancin kasar sannan magoya bayanta kan yi nuni da irin dumbin ilimi da take da shi a fannin diplomasiyya da siyasa a kasar ta Korea ta Kudu.

Cikin shekara 25, Yoo ta yi aiki a mukamai daban daban a ma'aikatun gwamnati inda ta samar da sauye-sauye tun bayan da ta ci jarabawar ma'aikata a 1991.

Hukumomin da jama'ar kasar ta Korea ta Kudu na mata kallon, "mai cike da dabara kuma gwana a fannin shiga tsakani."

A kuma bara ne shugaba Moon-Jae-in ya nada ta matsayin minista a gwamnatinsa.

A tsakanin ranakun 19-27 na watan Oktoba za a gudanar da zagayen karshe inda za a bayyana wacce za ta shugabanci hukumar tsakanin 'yan takatar biyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG