Duk da yin watsi da dattawan jihar Borno suka yi da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa akan daliban Chibok da aka sace, yanzu kwamitin din ya kai ziyara jihar ta Borno.
WASHINGTON, DC —
Bayan cika makonni biyar da aka sace 'yan matan makarantar sakandare dake Chibok kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa a karkashin shugabancin Janaral Ibrahim Sabo mai ritaya ta ziyarci jihar Borno.
'Yan kwamitin sun gana da duk ilahirin jami'an tsaro dake jihar a gidan gwamnatin jihar ta Borno. Janaral Ibrahim Sabo mai ritaya yace sun ziyarci jihar Borno ne domin su binciki yadda aka bar makarantar a bude har aka samu aka sace 'yan matan yayin da sauran makarantun jihar suna rufe. Zasu kuma nemi sanin ainihin kidiggigan 'yan matan da aka sace. Amma zasu yi aikin ne tare da jami'an tsaro da gwamnatin jihar. Suna son su san yawan daliban da suka samu kubuta kawo yanzu. Zasu fadakar da mutanen dake yankin da neman goyon bayan jama'a domin samun nasarar yadda za'a kubutar da 'yan matan.
Shugaban kwamitin yace ya kamata su yi magana da ganao domin su basu bayanin yadda abun ya faru. Daga karshe yace zasu ba gwamnatin tarayya shawara akan sharudan aikin da aka basu.
Kafin su isa jihar Borno sun tsaya a birnin Abuja inda suka yi wasu ayyuka da suka jibancin aikin da aka basu. Bayan jawaban shugaban kwamitin sai aka sallami 'yan jarida domin wai su gana a kebe da jami'an tsaro da na gwamnatin jihar.
Kada a manta cewa tun lokacin da aka kafa kwamitin dattawan Borno suka kalubali kwamitin. Mai magana da yawun kungiyar dattawan Borno Dr Bulama Malibu Byo ya kalubali kafa kwamitin wadda yace bashi da wani anfani garesu. Yace 'yan matan ba garuruwa daban daban suke ba. Wuri guda aka tafi da su domin haka gwamnati ta harzanta ta kubutar da su. Tun ba yau ba kungiyar Boko Haram ke kai hari makarantu kuma gwamnatin tarayya ta sani.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5