Magoya Bayan Gwamnan Naija Sun yi Tir da Kalaman Sanata Kuta

Gwamnan jahar Naija Ma'azu Babangida Aliyu

Jayayyar siyasa na dada yin kamari tsakanin gwamnan jahar Naija Babangida Aliyu da Sanata Dahiru Awaisu Kuta shi ma dan jahar ta Naija
Magoya bayan gwamna Ma'azu Babangida Aliyu na jahar Naija sun maida martani ga dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar gabashin jahar ta Naija Sanata Dahiru Awaisu Kuta game da kalaman da yayi na cewa gwamnatin Babangida Aliyu ta gaza wajen samar da ababen more rayuwa ga talakawan jahar. Magoya bayan gwamnan da suka maida wannan martani sun fito ne daga Kuta mazabar sanatan da yayi kalaman:

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Siyasa Tsakanin Gwamna Babangida da Sanata Kuta - 2:53


Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru batsari ne ya aiko da wannan rahoto daga Minna, jahar Naija.